ABNA24 : Majiyar muryar JMI ta nakalto Kenny Akinyemi kakakin tsohon shugaban kasar yana fadar haka a jiya litinin da yamma. Ya kuma kara da cewa tsohon shugaban zai shugabanci wata tawagar zuwa kasar ta Habasha don sasanta bangarorin biyu.
Sai dai gwamnatin kasar Habasha da kuma kungiyar Tarayyar Afirka sun ce basu san wanda ya dorawa Obasanjo wannan aikin ba.
A ranar 4 ga watan Nuwamban da muke ciki ne firai ministan kasar Habasha Abiy Ahmed su tura sojojin kasar zuwa yankin Tigray don murkushe yan tawaye a yankin.
342/